Za mu kara azawa Rasha takunkumi- Kerry

Sakataren harkokin wajn Amurka John Kerry Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakataren harkokin wajn Amurka John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi gargadin cewa idan Rasha bata shiga taitayinta ba za a kara garkama mata takunkumi.

Mr Kerry ya zargi kasar Rasha da zama sanadin karuwar tashe-tashen hankula a gabashin Ukraine.

Ya kuma ce Rashar ta gaza wajen cika hakkokinta karkashin yarjejeniyar da aka kulla a Geneva, inda take dora alhakin kan kasar Ukraine.

A baya dai ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta ce dole ne Amurka ta takawa mahukuntan kasar Ukraine birki su dakatar da amfani da karfin soji.

An dai umarci dakarun Rashar ne dake kan iyakar kasar Ukraine su gudanar atisaye.

Amma kuma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi gargadin cewa rikicin ka iya rincabewar da za a gaza shawo kan sa cikin sauki.