Sojoji: Mun kashe 'yan Boko Haram 40

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya rahotanni daga Jihar Borno, a arewa-maso-gabacin kasar, sun ce mutane 44 ne sun rasa rayukansu a wata aringama tsakanin sojoji da wasu da ake tsammanin cewa 'yan Boko Haram ne.

Rundunar sojin Najeriyar ta yi ikirarin kashe fiye da 'yan bindiga 40 yayinda sojoji hudu su ka rasa rayukansu a wajen aringamar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Chris Olukolade, ya bayar ta ce sojojin sun kama 'yan bindiga tara, sun kuma kwace makamai da dama.

To amma wani mazaunin garin ya yi ikirarin cewa wadanda aka kaman ba 'yan Boko Haram ba ne.

Ya ce sojojin sun je yankin ne sun kama mutane bayan 'yan bindiga sun riga sun kai hari, sun tsere.

Lamarin dai ya faru ne ranar Juma'a a garin Bulanbuli dake kan hanya tsakanin garin Alagarmo da dajin Sambisa inda ake tsammanin cewa can ne 'yan Boko Haram ke tsare da daliban nan 'yan mata da suka sace daga makarantar garin Chibok.

Karin bayani