INEC za ta fara rajistar masu zabe

Rajistar masu zabe a Najeriya
Image caption Rajistar masu zabe a Najeriya

A Najeriya hukumar zabe ta kasar wato INEC ta ce ta yi shirin fara aiki na ci gaba da yi wa masu zabe rajista a watan Mayu mai zuwa.

Hukumar ta INEC ta kuma karkasa jihohin kasar zuwa rukunnai ukku, don samun damar aiwatar da aikin cikin natsuwa da inganci tare da maganin matsalolin da aka fuskanta a irin wannan aiki a can baya.

Hukumar zaben ta Najeriya ta daddale cewa zata fara aikin ci gaba da yiwa masu zabe rajistar ne tun daga ranar 20 ga watan gobe na Mayu.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC Mr Nick Dazang ya shaidawa BBC cewa hukumar za ta ci gaba da yin rajista ga 'yan Najeriya da shekarunsu ya kai 18 tun zaben da aka yi na 2011 da basu samu sun yi ba.

A can baya dai irin wannan aiki ya yi fama da matsalolin da suka shafi na'urori da rashin gudanar da aiki yadda ya kamata.

Sai dai hukumar ta INEC a wannan karon ta dauki wasu matakai na gujewa sake abkuwar hakan.