Nigeria: An kashe mutane 34 a Nasarawa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ko baya ga wadanda suka mutu akwai wasu da dama da suka samu raunuka a rikicin.

Rahotanni daga jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya sun ce akalla mutane 34 ne suka mutu a cikin wani fadan kabilanci daya barke a wani kauye ranar Assabar.

Wani mai magana da yawun gwamnan jihar ya shaidawa BBC cewa fadan ya samo asali ne daga takaddama kan wata gona tsakanin kabilar Eggon ta mabiya addinin gargajiya na Ombatse da kuma kabilar Gwandara.

A cewar Alhaji Sani Musa Mairiga lamarin ya faru ne a kauyen Ega na karamar hukumar Nasarawa Eggon da ke arewacin jihar.

Ya ce dukkanin wadanda lamarin ya rutsa da su 'yan kabilar Gwandara ne. ''An tura jami'an tsaro sun can suna ta sintiri kuma komai ya lafa; amma ana iya gani gidaje da kayyakin amfanin gona suna ta konewa'' inji shi

Karin bayani