Lauyoyi sun yi barazanar kutsawa Sambisa

Chibok jihar Borno Najeriya Hakkin mallakar hoto
Image caption Chibok jihar Borno Najeriya

Kungiyar mata lauyoyi a Najeriya ta ce za ta kutsa dajin Sambisa don nemo 'yan matan nan 'yan makaranta da aka sace a garin Chibok dake jihar Borno kimanin sama da mako guda.

Matan Lauyoyi sun ce, sun yanke shawarar ne saboda jami'an tsaron kasar sun gaza daukar matakan ceto su.

Shugabar Kungiyar mata Lauyoyin ta Najeriya Hauwa Evelyn Shekarau ta shaidawa BBC cewa kungiyar na da matakai da dama da ta ke shirin dauka don ganin an sako 'yan matan.

Ta ce a shirye suke ko da kafa ne su je dajin na Sambisa don su roki wadanda suka yi garkuwa da su su sake su.

Hukumomi a kasar dai sun ce jami'an tsaro na can suna ci gaba da neman 'yan matan a cikin dajin da ake zaton an tafi da su.

A ciki da wajen Najeriya dai ana ci gaba da nuna matukar takaici dangane da yadda 'yan bindigar suka yi awon gaba da daliban mata sama da dari daya.