Obama ya ziyarci Malaysia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Malaysia na karbar bakoncin Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama yana ziyartar kasar Malaysia kwanaki biyu a ziyarar da yake yi a yankin Asia.

Shine dai shugaban kasar Amurka na farko da ya ziyarci kasar da take da rinjayen musulmai a shekaru arbain da takwas da suka wuce.

Shugaba Obama ya ce wannan wata sabuwar jituwa ce bayan shekaru da dama da dangantaka mai tsami.

Sai dai shugaba Obama zai fuskanci kalubale wajan tallata harkokin kasuwanci tsakanin kasashe ga 'yan kasar ta Malysia.

Obama zai ziyarci masallaci inda zai gana da Firai Minista Najib Razak.

Karin bayani