Prime Ministan Korea ta Kudu ya yi murabus

Prime Mintan Korea ta Kudu Chung Hung-Won Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Chung yace amsa kuwwar kukan iyalan yaran na hana shi bacci da daddare.

Prime Ministan Korea ta kudu ya yi murabus daga mukaminsa kan yadda gwamnati ta tafiyar da lamarin jirgin fasinjoji da ya nutse.

Chung Hong-won wanda yake cikin damuwa ya ce ci gaba da zama a ofis din wani babban nauyi ne da ya rataya a wuyansa, ya kuma bawa iyalan hakuri kan wannan bala'i da ya afka musu tare da cewa rashin maida hankali ya kara ta'azzara lamarin.

Ya kara da cewa kuwwar kukan da iyalan wadanda abin ya rutsa da su suke yi na hana shi bacci da daddare

Mr Chung an yi masa ihu a lokacin da ya ziyarci iyalan wadanda har yanzu ba a gan su ba, bayan anyi kwana daya da kifewar jirgin da har yanzu ba ayi bayanin musabbabin nutsewarsa ba.

Kusan mutane dari biyu sun mutu a hadarin kuma sama da dari har yanzu ba a gan su ba galibinsu 'dalibai da kuma Malamansu.

Har yanzu masu ninkaya na ci gaba da lalubar jirgin da ya nutse don gano wadanda suka bace, duk da cewa rashin kyawun yanayi da torokon teku na janyo cikas wajen aikin.