Tsoffin fafaroma sun zama waliyyai

Hakkin mallakar hoto Reuters

A wani bikin da ba'a taba ganin irinsa ba a fadar Vatican, Fafaroma Francis ya nada Fafaroma John na 23 da Fafaroma John Paul na biyu a mastayin waliyyai.

Kiristoci 'yan darikar Katolika da dama ne suka halarci bikin a birnin Rome.

Fafaroma Francis ya bayyana waliyyan da cewa bayin Allah ne wadanda su ka yi manyan ayyuka a duniya.

Ya kuma ce sun yi zamani ne a lokacin wasu bala'o'i a karni na 21.

Fafaroma Francis ya ambaci Fafaroma John na 23 a matsayin wanda ya kawo muhimman gyare-gyare a mujami'ar Katolika.

Ya kuma danganta Fafaroma John Paul na biyu da batun mutunta iyali.

Yace: "A ayyukan da yayiwa jama'a masu tsoron Allah, John Paul na biyu fafaroma ne na iyali. Shi da kansa yace ya na son a tuna dashi a matsayin fafaroman iyali.

"Ina farin cikin nuna hakan a lokacin da muke aikin sanya iyalai cikin tafarkin mujami'a".

Tsohon Fafaroma Benedict ma ya halarci bikin tare.

Wannan ne dai karo na farko da aka yi shelar sunayen fafaroma guda biyu a matsayin waliyyai.

Karin bayani