Obama na kamalla ziyararsa a Asia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama na ziyara a Phillipines

A yau Litinin ne shugaba Obama zai isa kasar Phillipines a rana ta karshe na ziyarar da yake yi yankin kudu maso gabashin Asia.

Ziyarar tasa ta zo daidai da lokacin da za a rattaba hannu kan wata yarjejeniyar harkokin tsaro tsakanin kasashen biyu, da za ta bada damar kara yawan sojojin Amurka a kasar ta Phillipines.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin Phillipines da China kan rashin daidaito a iyakokin kasashen biyu, haka kuma Amurka na da anniyar bawa yankin Manila tsauraran matakan tsaro.

Chris Hill tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka da suka shafi gabashin Asia da Pasific ya shaidawa BBC cewa kasashen biyu za su amfana da yarjejeniyar.

Karin bayani