'An ketara tafkin Chadi da 'yan matan Chibok'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyaye na cikin zaman zullumi

Kusan makonni da aka sace wasu dalibai 'yan mata a Chibok da ke jihar Borno, al'ummar yankin na zargin an tsallaka da wasu 'yan matan zuwa makwabtan kasashe.

Shugaban kungiyar cigaban al'ummar Chibok, Dr Pogu Bitrus a hirarsa da BBC ya yi zargin cewar sun samu labarin an tsallaka da wasu daga cikin 'yan matan ta tafkin Chadi.

Bitrus ya ce "Mun samu labarin cewar wasu daga cikin 'yan mata an tsallaka da su ta tafkin Chadi zuwa makwabtan kasashe".

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbarda wannan ikirarin.

Ya kara da cewar "Tunda aka sace 'yan matan daga makaranta, mun ji an kai wurare daban-daban. An kai wasu sambisa, wasu an tafi dasu gefen Dikwa, da kuma Marte da Monguno a arewacin Borno".

Dr Bitrus ya zargi jami'an tsaron Nigeria a kan cewar sun barsu cikin duhu game da lamarin.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Makonni biyu ba aji duriyar 'yan matan ba

Wakilin BBC ya tuntubi kakakin rundunar tsaro da ke jihar Borno wato JTF, Kanar Muhammed Dole amma ya ce baida hurumin yin magana sai dai a tuntubi Manjo Janar, Chris Olukolade a Abuja, wanda shi kuma muka yi ta kiran wayarsa amma ba a amsa ba.

'Rashin Tabbas'

Kwanaki goma sha hudu kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata 230 daga makarantar sakandiren gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno.

Wasu 'yan matan sun samu sun tsere, amma har yanzu ana zaman zullumi a garin saboda rashin sanin makomar wadanda har yanzu ke hannun 'yan bindigar.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babban Hafsan Dakarun Nigeria, Alex Badeh

Wasu rohotannin da ba a tabbatar dasu ba, sun ce anga wasu daga 'yan matan a wassu garuruwa da ke nesa da garin na Chibok, inda wata ta ce ta gansu a Gwoza.

Shugabannin al'ummar yankin na ganin cewar gwamnati ta gaza.

Dr Pogu Bitrus ya ce "Babu wanda ya san abinda gwamnati ke yi, don bamu ga komai a kasa ba, idan har suna wani abu to basu gaya mana ba. Iyaye na cikin bakin ciki a kan cewar akwai gwamnati amma kuma babu abinda aka yi don a kare musu 'ya'ya a makaranta".

Rundunar tsaron Nigeria a sanarwar da ta fita kwanakin baya ta ce tana iyaka kokarinta don ganin ta ceto 'yan matan.

A makon da ya gabata shugaba Jonathan ya tattauna da manyan jami'an tsaro, da gwamnonin jihohi inda ake ce wajibi ne a kubutar da 'yan-matan nan na Chibok.

Karin bayani