Chibok: Iyalai na ci gaba da zullumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen yaran na ci gaba da zullumi a Chibok

Kwanaki goma sha hudu bayan sace wasu dalibai 'yan mata a Chibok da ke jihar Borno, kawo yanzu ba a ji duriyar kusan 190 daga cikinsu ba.

Wani wanda kanwarsa da 'ya'yan 'yanuwansa suna cikin 'yan makarantar nan 230 da 'yan kungiyar d Boko Haram suka sace a Chibok ya fadawa BBC halin da iyalansa ke ciki.

Lawan wanda yake zaune a Abuja, babban birnin kasar ya ce yana yawan tuntubar 'yan uwansa ta wayar tarho domin jin inda aka kwana game da kokarin gano 'yan matan.

Wasu masu dauke da makamai ne suka yi awon gaba da 'yan matan daga dakunan kwanan su a ranar 14 ga watan Afrilu a garin Chibok da ke jihar Borno a arewacin Nigeria.

Image caption Lawan na cikin takaici

Har yanzu dai ba bu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin sace yan'matan.

'Takaici'

Duk lokacin da na kira 'yan uwa na a Chibok, hankali na tashi kuma ina kiransu sau biyu ko uku ko hudu kowacce rana, amma muna cikin tsaka mai wuya, wannan shi ne abinda Lawan ke cewa.

Kanwata shekarunta 15 ita ce kuma 'yar auta a gurin mahaifiyar mu.

'Ya'yan kanne na su biyu 'yan shekaru 12 da 13 ba wani abinda zan iya yi akai.

Matan 'yan uwa na sai kuka da bakin ciki suke yi, kamar yadda sauran mata ke yi.

Kafin wannan hari, ba a fiya samun hare-hare ba a Chibok.

An kone wani caji ofis kusan shekara daya da ta gabata, amma dai a iya cewa an cigaba da kasuwanci a hankali.

Karin bayani