An sauya tsarin neman jirgin Malaysia

Prime Ministan Australia Tony Abbot Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kassahen duniya da dama ne dai suka sanya hannu wajen lalubo jirgin da ya bata kwanaki hamsin da biyu da suka gabata.

Prime Ministan Australia Tonny Abbot ya ce an sauya fuskar tsarin neman jirgin Malaysian nan da ya yi batan dabo kusan watanni biyu da suka wuce.

Mr Abbot ya ce a yanzu babu tabbas na gano wasu daga cikin tarkacen jirgin da ake sa ran ganowa a tekun India, kuma za a fadada bincike a karkashin ruwa zuwa wani yankin.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta yi wa iyalan wadanda suke cikin jirgin alkawari, da kuma mutane da dama matafiya da cewa za ta yi duk yadda za ta iya dan ganin an kawo karshen wannan abu.

Ya na kuma so iyalan da kuma duniya su san cewa Australia ba za ta taba barin wannan aiki da ya rataya akanta ba.

Jirgin ruwa na karkashin kasa mai ganin kwakwaf zai ci gaba da aikinsa, ya yin da za a ba da kwantiragin binciken ga jiragen ruwa na fararen hula don su gwada sa'arsu.

Austalia dai za ta biya kudin aikin akalla dalar amurka miliyan sittin amma za ta bukaci taimakon kasashen duniya.

Binciken dai ka iya daukar wasu karin watanni kafin a gama shi, jirgin Malaysian dai ya bata ne kwanaki hamsin da biyu da suka gabata dauke da fasinjoji dari biyu da talatin da shida a lokacin da ya bata.