Za a kara yawan 'yan majalisa a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Shugaban Majalisar Dokokin Nijar, Hamma Amadou

Hukumomin Nijar sun ce sun amince a kara adadin 'yan Majalisar dokokin kasar daga dari-da-goma-sha-ukku zuwa 171.

Za a yi zaben karin 'yan majalisar 58 ne zabe mai zuwa da za a gudanar a kasar a shekara ta 2016.

Wannan kudirin na janyo kace nace a fagen siyasar kasar ganin irin dawainiyar da za a yi dasu daga aljuhun gwamnati.

Ministan harkokin wajen kasar kuma shugaban jam'iyyar PNDS mai mulki, Malam Bazoum Mohammed ya ce matakin kara yawan 'yan majalisar ya biyo bayan karin yawan al'ummar da aka samu a kasar ne.

Karin bayani