Cutar numfashi ta kashe mutane 102 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alamomin cutar sun hada da zazzabi da mura mai zafi da kuma cutar koda

Cutar numfashi da ke saurin kisa ta Mers ta kashe fiye da mutane 100 a Saudiyya, tun bayan bullarta a kasar a shekarar 2012.

Hukumomin lafiya na kasar sun ce wasu karin mutane takwas sun mutu a ranar Lahadin da ta wuce, hakan ya kawo adadin zuwa 102.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar na karuwa, yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO, ta nemi taimaka wa kasar ta hanyar binciken yadda ake kamuwa da cutar.

A ranar Asabar ne aka samu mutum na farko, wani mai shekaru 27 da ya kamu da cutar a Masar, bayan ya dawo daga Saudiyya.

Karin bayani