An sako mai sa ido da aka kama a Ukrain

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sako daya daga cikin wadanda aka kama a Ukrain

'Yan bindiga da ke goyon bayan Rasha a Ukarine sun sako wani dan kasar Sweden da ke cikin masu sa ido na kasashen duniya da 'yan bindigar suka kame su takwas a ranar juma'ar da ta gabata.

Ana ci gaba da kokarin sasantawa dan sako sauran mutane bakwan da har yanzu ba a sake su ba.

Tun da fari an nuna mutanen a wata tashar talabijin,a wani mataki da Ministan harkokin wajen Jamus ya bayyana da abu ne da bai dace ba.

Rasha ta amince kasashen OSCE su tura tawagar masu sa ido zuwa kasar Ukraine, sai dai wasu daga cikin masu sa ido da aka kama, Ukraine ce ta gayyato su zuwa babban birnin kasar ta Kiev.

Karin bayani