Ukraine: An harbi magajin garin Kharkiv

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr. Kernes na goyon bayan tsohon shugaban kasar, Viktor Yanukovych, amma ya daina saboda hadin kan Ukraine

Wasu 'yan bindiga sun harbi magajin garin kharkiv, Hennadiy Kernes a gabashin Ukraine, a ci gaba da tashe-tashen hankula da ke faruwa a yanki.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun harbe shi ne a baya, lokacin da ya fita motsa jiki, a halin yanzu ana yi masa aikin tiyata a asibiti.

Kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai na kokarin kakaba wa Rasha karin sabon takunkumi.

A ranar Litinin, wasu masu dauke da makamai, sanye da kaki sun kutsa ofishin gudanarwa na garin Kostyantynivka, inda suka daga tutar sabuwar "Jamhuriyar Donetsk".

Karin bayani