Wa'adin sulhu a Gabas ta Tsakiya ya kare

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kerry ya damu da rashin cimma yarjejeniyar sulhu

Wa'adin da Amurka ta bayar na cimma sulhu a gabas ta Tsakiya ya wuce ba tare da bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar ci gaba da tattaunawar ba.

Rashin cimma daidai ton ya samu ne yadda Plasdinawa ke nuna fushi kan ke ma ga das das da Israela tayi na kin sakar fursunoni da kuma kin yarda da gwamnatin hadin kan kasa da Kungiyar Hamas.

Ci gaba da gina matsugunan Yahudawa da Israela ke yi ya na bakantawa Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry rai gami da kuma yunkurin da Palastinawa ke yi na yin gwamnatin hadin kan kasa da Kungiyar Hamas.

Amma John Kerry bai amince ya kasa cimma burinsa ba na sulhu sai yake amfani da kalmomi kamar dan tsaiko a tattaunawar sulhu, wata dabara na nuna cewa za a ci gaba da tattaunawar.

Akwai yiwuwar Amurka za ta rika duba ci gaban da aka samu zuwa wani lokaci yayinda take ci gaba da azamar a dawo ci gaba da tattaunawar.

Karin bayani