Chibok: Muna aiki cikin sirri ne - sojoji

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hedkwatar sojin Nigeria ta bukaci a taya ta addu'a a aikin da take yi na ceto 'yan makarantar Chibok

Hedkwatar tsaron Nigeria ta ce ayyukan da take yi domin ceto 'yan makarantar Chibok sirri ne.

Kakakin hedkwatar, Manjo Janar Chris Olukolade, ya shaidawa BBC cewa kodayake sun fahimci irin damuwar da mutane ke ciki game da halin da 'yan makarantar ke ciki, amma suna yin kokari wajen ceto su.

Ya kara da cewa duk bayanan da suke samu game da yadda za a gano 'yan makarantar suna yin amfani da su, duk dai da zummar samun nasara.

Hedkwatar tsaron ta bukaci 'yan kasar su ci gaba da yi mata addu'a a yunkurin da take yi na farauto matan.