Chibok: Iyaye mata sun yi gangami a Abuja

Image caption Rundunar tsaron Nigeria ta ce tana ayyukan ceton 'yan matan cikin sirri ne

Wasu iyaye mata sun yi gangami a dandalin Eagle Square da ke Abuja, suna neman Shugaba Goodluck Jonathan ya yi musu bayani game da yunkurin kubutar da 'yan matan Chibok.

Matan kimanin 30 'yan asalin Chibok mazauna Abuja, sun ce ba su gamsu da kokarin da gwamnatin Nigeria ta ce tana yi ba, wajen kubutar da yaransu.

Wacce ta jagoranci gangamin Mrs Naomi Mutah ta ce "Wasu iyaye mata na can na fama da hawan jini, wasu na kwance a asibiti, saboda halin rashin tabbas game da 'ya'yansu."

Kwanaki 15 kenan da wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai matan kusan 200 daga wata makarantar sakandare da ke garin Chibok a jihar Borno.

Karin bayani