Maza na iya auren mata da yawa a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ya sanya hannu a kan dokar da za ta baiwa maza damar auren mace fiye da daya.

Dokar na shan suka daga kungiyoyin addinnin Kirista da kuma kungiyoyin mata a kasar.

A watan da ya gabata ne Majalisar dokokin Kenya ta zartar da dokar wacce ke bin tsarin gargajiya.

Mata 'yan majalisa sun fice daga zauren majalisar bayan zazzafar mahawara kan batun.

Kungiyar mata lauyoyi a kasar ta ce za ta kalubalanci matakin a gaban kuliya.

Karin bayani