Rasha ta yi Allah wadai da Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Putin da Shugaba Obama

Rasha ta yi Allah wadai da sabbin takunkumin da Amurka da Tarrayar Turai su ka kakaba mata a kan batun yinkurin kawo har gitsi a Ukraine.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Ryabkov ya ce takunkumin na Amurka zai iya kawo cikas a bangaren fasahar zamani na kasar ta Rasha.

Moscow kuma ta ce kungiyar tarrayar Turai- EU ta zama 'yar korar Washington kuma ta yi abun kunya.

Tun da farko, kungiyar ta EU ta ce sabon takunkumin zai shafi wasu mutane 15 a Rasha ciki hadda Mataimakin Firaminista.

Masu lura da al'amura sun ce mutanen da kungiyar EU ta kakaba wa takunkunmi ba su yi fice kamar mutane 17 da Amurka ta kakaba wa takunkumi.

Karin bayani