Navy Pillay na ziyara a Sudan ta kudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Navy Pillay na ziyara a Sudan ta Kudu

Babbar Jamiar Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navy Pillay, ta na Sudan ta Kudu don duba yadda alamurra suka kasance bayan kusan watanni hudu da aka shafe ana zubar da jini wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

kisan daruruwan mutane da akayi makon da ya gabata na fararan hula a garin Bentiu, yankin dake da arzikin man fetur ya jawo koke koken kasashen duniya.

Wani rahoto mai dimautarwa da Kungiyar likitocin bada agajii na Medicine san frontier ta fitar ta bayyana kisan a matsayin wani rikici mai rikitarwa tun lokacin da fada ya barke a kasar da ta zama mai cin gashin kanta a watan Disambar bara.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi yan adawa da kisan amma sun musanta wannan zargi.

Pillay za kuma ta hadu da wasu mutane da rikicin ya daidaita kuma za ta yi magana da shugabannin alummomi.

Karin bayani