Al'ummar Sudan ta Kudu na tsaka mai wuya

Image caption Mutane kusan miliyan daya sun rasa muhallansu.

Wani rahoton da ya duba kasashe, inda jama'a suka fi fuskantar barazanar tashin hankali, ya sa Sudan ta Kudu a matsayin kasar da al'amurra suka tabarbare matuka a cikin shekarar da ta gabata.

Binciken, wanda aka yi wa lakani da 'Al'ummar da ke fuskantar barazana' ya kuma saka Jamhuriyar tsakiyar Afrika, da Syria da Yemen a wannan sahu.

Rikicin kabilanci dai na ta karuwa a Sudan ta kudu, kuma har yanzu babu wata alama ta samun ci gaba a shawarwarin zaman lafiya.

Wani rahoto da Kungiyar Likitoci ta Medicins Sans Frontiers ta fitar, ya bayyana irin mummuna tashin hankali da kisan gilla da ake yi a kasar.

'Yan kabilar Nuer dauke da makamai na kisa a asibiti da coci da masallatai sannan suna watsa jawabai na nuna kiyayya ta kafofin yada labarai, inda suke tunzura mutane kaiwa wasu hari tare da aikata fyade.

A yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe a Sudan ta Kudu, sannan suma shawarwarin neman zaman lafiyar suka cije, rikicin a tilastawa mutane fiye da miliyan guda barin gidajensu.

Karin bayani