Mata sun yi zanga zanga a Abuja

Wasu mata masu zanga zanga Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mata masu zanga zanga

Wasu kungiyoyin mata sun yi zanga zanga a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria, suna neman gwamnati ta kara tashi tsaye kan neman 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a jihar Borno.

Duk da ruwan sama, kamar da bakin-kwarya, daruruwan mata sun yi maci zuwa Majalisar Dokoki ta kasa, inda suka mika wasika ga shugaban majalisar dattawa.

Suna nema ne a kara daukar matakai na kubutar da 'yan mata sama da dari da yau sama da makonni biyu kenan suna hannun 'Yan Boko Haram da suka sace su.

Shugaban majalisar dattawan, David Mark yayi alkawarin duba bukatun nasu.

A daya bangaren, ministan harkokin Cikin gida Abba Moro ya ce gwamnati na yin iya kokarinta domin gani ta kubutar da 'yan matan.

Can ma a Kano, an gudanar da irin wannan zanga zanga.