Ana zabe cikin matakan tsaro a Iraqi

Image caption Ba za a gudanar da zaben a lardin Anbar ba saboda ayyukan masu fafutuka

Dubban jami'an soji da 'yan sanda ne ke gadin rumfunan zabe a kasar Iraqi, inda ake gudanar da zaben 'yan majalisar kasar.

Firai ministan rikon kwarya na kasar, Nouri al-Maliki na neman wa'adi na uku, amma zaman dar-dar da rikice-rikice da ake fama da shi a wasu bangarorin kasar ya mamaye yakin neman zaben.

An dai sa dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a birnin Baghadaza, inda al-Maliki ya kada kuri'arsa a wani otel.

Babban zaben shi ne na farko tun bayan ficewar dakarun Amurka daga kasar a shekarar 2011.