Chibok: Mata za su yi gangami a Nigeria

Matan da za su yi gangami a Abuja.
Image caption Gangamin wanda kungiyar Women For Justice and Peace za ta jagoranta zai bukaci gwamnati ta kara kaimi

A ranar Laraba wata kungiyar mata za ta jagoranci gangami na mata miliyan daya a Abuja, domin matsin lamba ga gwamnatin Nigeria game da ceton 'yan matan Chibok.

Za a fara gangamin ne da misalin karfe uku na yamma agogon kasar, inda matan za su yi jerin-gwano zuwa majalisar dokoki.

Haka kuma za su je ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, domin mika wasiku zuwa ga shugaban kasa.

Haka zalika za a yi irin wannan gangamin a wasu jihohin arewacin kasar, ciki har da Kano wadda ta fi kowace jiha yawan al'umma a kasar.

Kwanaki 16 kenan tun da wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace 'yan makarantar a garin Chibok.