An dauki yara mayaka 9000 a Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijiran Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin mutane miliyan daya ne suka rasa matsugunansu, saboda rikicin

Fiye da yara 9000 ne a ka dauka a matsayin mayaka, a mummunan tashin hankalin da ake yi a Sudan ta Kudu.

Shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navy Pillay ta ce sojojin gwamnati da 'yan tawaye duka na daukar kananan yaran, domin yaki.

Ms Pillay ta ce kasar kuma na fuskantar barazanar fari, amma ga dukkan alamu shugabannin ba su damu ba.

A watan Disambar bara ne tashin hankali ya barke tsakanin masu goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Hakan ya biyo bayan zargin da Mr. Kiir ya yi na cewa Riek ya yi yunkurin yi masa juyin mulki.