An gano karin abubuwan fashewa uku a Nyanya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lamarin ya jefa tsoro a tsakanin al'ummar Nigeria

'Yan sanda a Nigeria sun ce sun gano wasu abubuwan fashewa uku a kusa da inda wani bam ya fashe a Nyanya da ke Abuja, lamarin da ya janyo mutuwar mutane 19.

Kwamishinan 'yan sanda a Abuja, Mbu Joseph Mbu ya ce an samu damar kwance abubuwan kafin su fashe.

Fashewar bam din a Nyanya a ranar Alhamis ya zo ne kusan makonni biyu bayan da wani bam din ya fashe a tashar mota ta Nyanya inda mutane kusan 75 suka mutu.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin da aka kai a watan Afrilu.

Tashin bama-baman na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da neman 'yan mata fiye da 200 da aka sace a wata makarantar kwana da ke Chibok a jihar Borno.

Karin bayani