Chibok: Gangami a fadin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen yara na cikin zullumi

Iyayen 'yan mata 230 da aka sace a wata makaranta da ke Chibok a jihar Borno sun yi maci zuwa harabar makarantar domin neman a taimaka a gano musu 'ya'yansu.

Kwanaki goma sha bakwai kenan da aka je cikin dare aka sace 'yan mata a makarantar sakandaren kwana da ke Chibok a jihar Borno na arewa maso gabashin Nigeria.

Daya daga cikin iyayen wacce ba ta son a bayyana sunanta ta gode wa 'yan Nigeria bisa goyon bayan da suka bayar don ganin an ceto 'yan matan da aka sace.

Kawo yanzu dai kungiyar Boko Haram wacce ake zargin ita ce ta sace 'yan matan, ba ta bayyana dalilanta na yin hakan ba.

A wani matakin matsawa gwamnatin Nigeria lamba don ganin ta tashi tsaye, an gudanar da gangami a jihohin daban daban na kasar.

An yi gangami a jihar Kaduna da Kano da Lagos da kuma Abuja babban birnin kasar.

Karin bayani