A tsaurarawa 'yan ta'adda- Xi Jinping

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an gwamnati sun ce wasu mutanen ma an yayyanke su ne da wuka.

Shugaban China Xi Jinping ya yi kira da a dauki tsattsauran mataki a kan wadanda ya bayyana a matsayin 'yan ta'adda.

Shugaban na magana ne bayan fashewar wani bam da ya hallaka mutane uku ranar Laraba a yankin Xinjiang da ke fama da rikici.

Bam din da ya tashi a wata tashar jirgin kasa a Urumqi, ya kuma raunata wasu mutanen kusan tamanin.

An dai kai harin ne yayin da shugaban Chinan ke kammala ziyara a yankin na Xinjiang, wanda ya yi fama da rikicin addini da na kabilanci da ya hada da al'ummar musulmin yankin 'yan kabilar Uighur.