Ireland ta Arewa: An kama Gerry Adams

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Sinn Fein ta yi Allah-wadai da kama shi tana cewa kamun na da alaka da siyasa.

'yan sanda sun kama daya daga cikin manyan 'yan siyasar Ireland ta Arewa, jagoran kungiyar Sinn Fein, Gerry Adams, kan zargin kisan wata mata.

Ana masa tambayoyi ne dangane da kisan Jean McConville, wadda kungiyar 'yan aware ta IRA ta sace a gaban 'ya'yanta tun 1972.

Tsawon shekara da shekaru ba a gano inda gawarta take ba.

Shi dai Mr Adams ya musanta hannu a kisan, kuma ya ce bisa radin kansa ne, ya gabatar da kansa ga 'yan sandan don su masa tambayoyi.