An zartar da dokar hana acaba a Kaduna

  • 1 Mayu 2014
Image copyright KDGH
Image caption Kudin dokar na gaban, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria ta zartar da kudurin dokar hana haya da babura ko kuma acaba a cikin jihar.

Majalisar ta zartar ta kudurin ne bayan shafe watanni shida ta na nazari kan batun.

Bayanai sun nuna cewar matakin majalisar ya biyo bayan la'akari da matsalolin tsaron da ake fama da su a jihar sanadiyyar kaurar 'yan achaba daga makwabtan jihohi da aka haramta haya da babura ko kuma okada.

Rahotanni sun nuna cewar wasu daga cikin 'yan acaban daga makwabtan jihohi na kwana ne a kasuwanni da kangwaye da tashoshin motoci.

A yanzu dai majalisar ta mika wa gwamnan jihar wannan kudurin dokar domin sanya hannu.

Kudurin dokar dai ya tanadi tara ko dauri ko dukka ga wanda ya saba.

Tuni jam'iyyar APC mai adawa a Kaduna ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga gwamnan jihar da kada ya sanya hannu a kan kudurin dokar.

Karin bayani