Gangami ya mamaye ranar ma'aikata

Image caption Daruruwan mata da wasu maza da suka yi gangami kan sace 'yan matan Chibok

Yayin da ake bikin ranar ma'aikata ta duniya, wasu al'ummar Nigeria sun yi amfani da ranar domin yin gangami kan batun sace 'yan matan Chibok.

Daruruwan mata da maza ne suka yi irin wannan gangamin, a ranar Alhamis a garin Chibok da jihar kaduna da Lagos, yayin da za a sake yin gangami a Abuja.

Batun sace 'yan matan sama da 200 a garin Chibok na ci gaba da jan hankali ba a Nigeria kadai ba, har ma da kasashen duniya.

Hakan na zuwa ne yayin da ita ma daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago a Nigeria, wato NLC ta shirya gangami a jihohin fadin Najeriya da kuma babban birnin tarayyar Abuja.

Daya ga watan Mayu ce ranar ma'aikata ta duniya, wadda aka kebe a kowace shekara, domin yin nazari kan irin gwagwarmayar da ma'aikata ke yi da kuma irin kalubalen da suke fuskanta.