Nigeria: 'Bam' yayi ta'adi a Nyanya

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya rahotanni daga Abuja na cewa, wani abu da ake kyautata zaton bam ne yayi ta'adi a unguwar Nyanya a kusa da wurin da cikin makonnin baya aka kai harin bam da ya halaka mutane saba'in da daya.

Wani shaida a wurin ya fadawa BBC cewa, bam din ya halaka mutane da dama kuma ana ci gaba da kwashe gawarwakin mutane da kuma wadanda bam din ya jikkata.

Yanzu haka dai jami'an tsaro sun garzaya wurin, kuma motocin hukumar bada agajin gaggawa suna ci gaba da kwashe mutanen da suka jikkata.

Mazauna unguwar suna cewa, abinda ya fashe din ya girgiza gidajen unguwar, kuma mutane sun kidime sosai.