Nyanya:Mutane 19 sun mutu, 60 sun raunata

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin an dasa bam din ne a cikin mota

Hukumomi a Nigeria sun tabbatar da mutuwar mutane 19 a yayinda wasu 60 suka samu raunuka sakamakon tashin bam a Nyanya da ke Abuja.

Bam din ya tashi ne a ranar Alhamis da daddare kusa da tashar motar da mutane 75 suka mutu sakamakon tashin wani bam din a ranar 14 ga watan Afrilu.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma Boko Haram ta dauki alhaki kai harin bam din watan da ya gabata.

Mazauna unguwar suna cewa, abinda ya fashe din ya girgiza gidajen unguwar, kuma mutane sun kidime sosai.

Malam Badamasi Mohammed wani mazaunin Nyanya din ya ce " Na ga gawarwaki da dama, motar NEMA ta yi sawu biyu na gawarwaki".

Harin na zuwa ne kwanaki kadan kafin Abuja ta dauki bakuncin taron tattalin arziki na duniya a kan Afrika.

Rashin tsaro babbar matsala ce a Nigeria, sannan shugabannin kasashen duniya za su halarci taron ciki hadda Firaministan China, Li Keqiang.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai wadanda suka samu raunuka asibitin Asokoro
Hakkin mallakar hoto google
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Motoci da dama sun kone

Karin bayani