Sony ya yi hasashen tafka hasara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sony na fuskantar kalubale a kasuwar lataroni

Kamfanin Sony na kasar Japan mai kera kayan lantarki ya ce zai fitar da rahoton faduwar da ya samu fiye da yadda ya yi hasashe a bara sakamakon karin kudaden da ya kashe saboda fice wa daga hada-hadar sarrafa kayayyakin kwamfyutarsa na Vaio.

Kamfanin ya kuma yi hasara sakamakon kudaden da aka caje shi kan faduwar darajar faya-fayan disc dinsa, musammam na Blu-Ray DVD.

Katafaren kamfanin a yanzu yana sa ran ba da rahoton faduwar da ta kai $1.3 biliyan a daukacin shekarar kudi ta bara.

A watan Fabrairu, Sony ya ce yana iya yin hasarar da ta kai tsabar kudi yen biliyan 110.

Don haka kamfanin ya daidaita kudaden gudanar da za a kashe a matsayin yen biliyan 26, ragi mai girma daga yen biliyan 80 da ya yi hasashe kashewa a watan Fabrairu.

Babban dalilin hakan kuma shi ne karuwar kudaden da yake kashewa wajen sake fasalin kamfani.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Sony ya ce zai kuma yi hasarar karin yen biliyan 30 a kan kudaden da yake kashewa don fita daga hada-hadarsa na sarrafa kayayyakin kwamfyuta.

Sony ya ce kasuwar kayayyakin nadar bayanai ta ragu cikin hanzari fiye da yadda aka yi hasashe.

Ya kuma sanar a watan Fabrairu cewa zai cefanar da masana'antar sarrafa kayayyakin kwamfyuta, zai kuma raba bangaren sarrafa akwatunan talabijin zuwa masana'anta mai zaman kanta a yunkurin sake fasalin kamfani.

Raba bangarorin sarrafa Talabiji da kwamfyutocin wani babban koma-baya ne ga kudaden shigar kamfanin Sony a shekarun baya-bayan nan.

Karin bayani