An yi sulhu da 'yan tawayen Homs na Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dubban mutane sun mutu a Homs

An cimma wata yarjejeniya tsakanin dakarun gwamnatin Syria da 'yan tawaye a birnin Homs.

Hakan zai baiwa mayakan 'yan adawa su janye daga wurarensu.

Kungiyar kula da kare hakkin bil adama ta Syria ta ce, mayaka kusan 1,000 ne ake sa ran za su bar birnin a cikin sa'o'i 48 masu zuwa.

An yi wa birnin kawanyar da ta kwashe shekaru biyu ne domin mayakan 'yan tawayen da aka yi wa kofar raggo a ciki da zagayen tsohon birnin.

A halin da ake ciki kuma gidan talabijin na Syria ya bayar da rahoton cewar mutane akalla 18 ne hade da yara kanana da yawa aka kashe a wasu hare-haren bama-bamai na dabam da aka kai da wata mota a kauyuka biyu a lardin tsakiyar kasar na Hama.

Karin bayani