An kai farmakin soji a gabashin Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Ukraine sun doshi gabashin kasar

Dakarun Ukraine na gudanar da wani farmakin soji a kan 'yan gwagwarmayar da ke goyon bayan Rasha a birnin Sloviansk na gabashin kasar.

Yuriy Povkh, wani mai baiwa Ministan tsaro na Ukraine shawara ya ce 'yan awaren na dauke da manyan makamai ne.

Ya ce "Dakarun da ke yakin fatattakar 'yan ta'adda na fuskantar tirjiya daga masu zagon kasa da 'yan ta'addan da ke dauke da nagartattun makamai da cikakken horo da kuma cikakken shiri".

Gwamnatin Ukraine ta ce an harbo jiragen sama masu saukar ungulu biyu na Ukraine da makamai masu iya kakkabo jiragen sama kuma an kashe daya daga cikin matukan jiragen.

Hukumomi a Kiev sun ce dakarunsu sun kwace iko da wuraren duba ababen hawa da yawa.

Wani shugaban sojin sa kan masu goyon bayan Rasha sunce an yi artabu a kusa da tashar jirgin kasa.

Karin bayani