Chibok: Amurka za ta taimakawa Nigeria

Najeriya Chibok Boko Haram Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Najeriya Chibok Boko Haram

Amurka ta ce za ta taimakawa Najeriya wajen farauto 'yan matan Chibok da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace a makarantarsu da ke jihar Borno.

Amurkar ta bayyana aniyar bayar da gudumawar ta wajen ganin cewa yunkurin da hukumomin Najeriyar ke yi na ceto 'yan matan daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram ya kai ga nasara.

Mai magana da yawun ofishin huddar jakadancin Amurkar Marie Harf ta shaidawa manema labarai cewa Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da kuma taimakawa ta duk hanyar da zata iya.

Sai dai Ms Harf bata bayyana ko wane irin taimako ne Amurkar za ta baiwa Najeriyar ba, amma kuma ta ce sun san da cewa Kungiyar Boko Haram ta kara bunkasa a arewacin kasar musammam arewa maso gabas.

Ta wani gefen kuma wasu sanatocin Amurkar sun gabatar da wani kudiri dake yin Allah wadai da sace 'yan matan.

Sun kuma yi kira ga gwamnatin Amurkar da sauran kasashen duniya su tallafa wajen gudanar da ayyukan ceton su.