Jonathan zai gana da wasu jami'an Borno

Hakkin mallakar hoto Getty

Fadar shugaban Najeriya ta gayyaci wasu jami'an gwamnatin Jihar Borno domin yin wata tattaunawa ta musamman akan batun dalibai matan nan da aka sace.

Cikin wadanda aka gayyata harda kwamishinan ilmi, Alhaji Musa Inuwa Kubo, da kuma shugabar makarantar sakandiren Chibok.

A yau ne jami'an gwamnatin da aka gayyatar zuwa fadar shugaban kasar za su isa Abuja.

Yau kusan makonni ukku kenan tun bayan da aka sace 'yan mata sama da 200 daga makarantar sakandiren gwamnati dake garin Chibok, a jihar Borno.