'Za mu gano 'yan matan da aka sace'

  • 4 Mayu 2014
Image copyright Getty

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayi alkawalin cewa za su gano 'yan matan nan da aka sace a makarantar sakandiren Chibok duk inda suke.

Shugaban ya kuma ce mai yiyuwa a tsawaita dokar ta-bacin da aka kafa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Ya fadi haka ne a tattaunawar da ya yi da 'yan jaridu a Abuja, wadda aka nuna kai tsaye a gidajen telebijin na kasar.

Karin bayani