Najeriya:An hana Sanusi Lamido fita waje

Sanusi Lamido tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya
Image caption Sanusi Lamido tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya

Jami'an tsaron farin kaya a Nigeria sun hana tsohon gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi fita waje, bayan sun kwace masa fasfo.

Sanusi Lamido ya shaidawa manema labarai a filin jirgin saman Malam Aminu Kano cewa jami'an tsaron sun kwace fasfo din na sa ne yayin da yake shirin fita zuwa Paris a daren Lahadi.

Ya kuma ce zai kalubalanci wannan matakin da ya bayyana na tauye masa hakki a gaban kotu.

A watan jiya ne dai wata kotu a kasar ta hana gwamnati da jami'an tsaron Nigeria daukar duk wani mataki a kan sa da suka hadar da hana shi futa waje.