Dakarun Sudan ta Kudu sun kame Bentiu

Hakkin mallakar hoto Reuters

Dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu sun karbe iko da garin Bentiu mai muhummanci.

Sun fattaki dakarun 'yan tawaye ne daga wani sansanin su da 'yan tawayen suka kame a watan jiya a wata karawa.

Wani wakilin BBC a garin na Bentiu ya ce yaga dakarun gwamanti da kuma motoci masu sulke na shiga garin. Ya kuma bada labarin karar harbe-harbe.

Karawar ta zone ne kwanaki biyu bayan shugaba Salva Kir ya shaidawa sakataren harkokin wajen Amurka cewa a shirye yake ya tattauna da shugaban 'yan tawayen, Riek Machar.