Ukraine: Zaman zullumi ya karu a birnin Odessa

Damuwa a birnin Odessa gabashin kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Damuwa a birnin Odessa gabashin kasar Ukraine

Fargaba ta karu a birnin Odessa kasar Ukraine, inda aka kashe mutane 42 yayin arangama tsakanin magoya bayan Rasha da na gwamnatin Ukraine.

Akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a cikin wutar da ta tashi a ginin kungiyar ma'aikata inda masu zanga-zangar goyon bayan Rashar suka yi ka-ka gida.

An dai yi ta jefa bama-baman da aka hada da petur ne kan ginin.

Wakilin BBC a birnin Odessa ya ce, mutuwar mutanen ta haifar da tda damuwa a tsakanin masu magana da harshen Rashanci da daruruwansu suka hallara a wurin da wutar ta kama ranar Asabar.

Mai magana da yawun shugaba Putin na Rasha Dmitry Peskov ya zargi gwamnatin wucin gadi a birnin Kiev da ingiza masu tsatsauran kishin kasar wajen aikata kisan, inda ya ce an yi ta samun kiran neman dauki daga dubannin magoya bayan kasar Rashar dake gabashin Ukraine.

Ministan harkokin kasashen wajen Jamus Frank-Walter ya ce, abkuwar lamarin ya nuna yadda halin da aka shiga zai iya kaiwa yadda za a kasa shawo kan rikicin.