Niger: 'Yan cirani 20 sun rasu a hamada

Yan cirani a Janhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan cirani da suka rasu a cikin hamada

A Jamhuriyar Nijar wasu mata da kananan yara sama da 20 yan asalin yankin Matamey,sun rasa rayukansu a cikin hamada sakamakon kishin ruwa da yunwa yayin da suke kokarin ketarawa zuwa kasar Algeria.

Lamarin ya faru ne a ranar juma'ar da ta gabata bayan da direban da ya dauke su daga Arlit ya zubar da su a cikin kungurmin daji.

Wata mata dake cikin 'yan cirani ta ce su shida ne kawai suka tsira bayan wata mota dake wucewa ta kawo masu dauki.

Ko a watannin da suka gabata dai wasu yan asalin yankin na Matamey 92 sun rasa rayukansu a cikin hamadar a kan hanyarsu ta zuwa Tamaraset.

Hukumomin Niger sun dau matakan rufe gidajen sauke baki domin magance matsalar sai dai matakan ba su yi tasiri ba.

Karin bayani