Mu muka sace 'yan matan Chibok - Shekau

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace 'yan mata dalibai 276 daga wata makarantar sakandare a Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyo da ya fitar a ranar Litinin ya ce "Ni na sace 'yan matan".

Hakan na zuwa a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa ke kara matsin lamba a kan batun sace dalibai 'yan matan su 276 kusan makonni uku da suka wuce.

Kawo yanzu 'yan mata 53 sun kubutu daga hannun 'yan Boko Haram, kenan akwai sauran 'yan mata 223 a hannun 'yan Boko Haram.

Iyayen dalibai 'yan matan sun bayyana takaicinsu na jiran gawon shanun labarin halin da 'ya'yansu ke ciki.

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan mai suna Martha Yarama Ndirpaya ta zargi gwamnatin kasar da kin bayyana gaskiya da taimakawa wajen gano 'ya'yan su.

Karin bayani