'Boko Haram' sun kai hari Gamboru Ngala

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram sun kashe mutane da dama cikin wannan shekarar

Rahotanni daga Nigeria na cewa, wasu da ake zaton 'yan Boko Haram sun kai mummunan hari a garin Gamboru Ngala dake kan iyakar Nijeriya da Kamaru.

Wasu mazauna garin sun ce, an kashe mutane da dama, kuma an kona kasuwar garin yayin da ta ke ci yau Litinin.

Yayin harin wani mazaunin garin yace, 'yan Boko Haram din sun kuma yi awon gaba da dimbin kayan abinci.

Mazauna garin da dama sun tsallaka zuwa Kamaru domin tsira da ransu.

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin cewa, ita ta sace, 'yan mata fiye da 200 daga garin Chibok.boko haram