Hakuri ne zai kai mu ga ci - Rodgers

Hakkin mallakar hoto barclays premier league
Image caption Rodgers da 'yan tawagarsa na haskakawa a Ingila

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya ce hakuri shi ne abinda zai taimakawa kungiyar ta kai matakin da take bukata a fagen kwallon kafa.

Liverpool za ta kara da Crystal Palace a ranar Litinin, bayan da Chelsea ta kawo mata cikas a kokarin ta na lashe gasar Premier a karon farko cikin shekaru 24.

Rodgers yace "Mun kasa hakuri a wasanmu da Chelsea a don haka muna bukatar hakuri don kaiwa ga samun nasara".

A halin yanzu dai Manchester City ce ke jan ragamar gasar Premier saboda ta fi Liverpool zura kwallaye.

Sakamakon wasannin Premier na karshen mako:

*West Ham 2-0 Tottenham *Aston Villa 3-1 Hull *Man Utd 0-1 Sunderland *Newcastle 3-0 Cardiff *Stoke 4-1 Fulham *Swansea 0-1 Southampton *Everton 2-3 Man City

Karin bayani