Samsung zai biya Apple diyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Apple da Samsung sun dade suna takun saka

Wata kotu a Amurka ta umarci kamfanin Samsung ya biya Apple diyyar $119.6 miliyan saboda saba ka'ida kan hakkin mallaka.

Ayarin masu taya alkali hukunci a kotun tarayya ta San Jose da ke California ne ya gabatar da wannan shawara ranar Juma'a a shari'ar baya-bayan nan tsakanin manyan kamfanonin kera wayoyin salula.

Kamfanin Apple ya nemi a biya shi diyyar dala biliyan 2 a wannan shari'a, bayan ya zargi Samsung da shiga iyakar hakkin mallakar fasahohin wayar salularsa na zamani da suka shafi yadda wayar salularsa ke aiki kamar "kullewa idan an ja labulen wayar".

Haka zalika, kotun ta yanke hukuncin cewa shi ma Apple ya keta haddin Samsung don haka ya biya shi diyyar dala dubu 158.

Samsung dai ya musanta aikata ba daidai ba, kuma ya bukaci a biya shi dala miliyan shida bayan ya ce lallai-i-lalla kamfanin Apple ya shigar masa iyaka ta hanyar kwaikwayon fasahohinsa biyu da suka danganci amfani da kyamara da aika wa da hotunan bidiyo.

Wani malamin shari'a a Jami'ar Santa Clara, Brian Love ya ce "ko da yake hukuncin wani gagarumin abu ne, sai dai da wuya a iya kallonsa a matsayin wata nasara ga Apple".

Ya ce "kudin bai fi kaso 10 cikin 100 na diyyar da Apple ya nema ba, kuma mai yiwuwa da kadan diyyar ta fi kudin da ya kashe a kan wannan shari'a".

Wannan hukunci wata manuniya ce ta gwagwarmayar shari'a ta baya-bayan nan a kan hakkin mallaka tsakanin manyan kamfanonin biyu masu kera wayoyin salula na zamani.

Kamfanonin Apple da Samsung na ta kai ruwa rana tsawon shekaru a kan batun satar fasaha a kasashe da dama.

Shekaru biyu da suka gabata, sai da wata kotu ta bai wa Samsung umarnin biyan Apple dala miliyan 930 bayan samun kamfanin da laifin yin amfani da fasahar Apple, ko da yake har yanzu Samsung na ci gaba da kalubalantar wannan hukunci.

Karin bayani