Jami'ar Al-Azhar ta yi fatawa kan Boko Haram

Image caption Jami'ar Al-Azhar cibiya ce ta Musulunci a duniya

Babbar jami'ar Islama ta Al-Azhar da ke Masar ta ce ayyukan kungiyar Boko Haram sun sabawa koyarwar addinnin Musulunci.

Jami'ar Al-Azhar wacce ke bin mazhabar Sunni ta bukaci 'yan Boko Haram su sako 'yan matan da suka sace ba tare da bata lokaci ba.

A ranar 14 ga watan Afrilu 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai 276 a wata makaranta a Chibok da ke jihar Borno.

Wasu daga cikin 'yan matan sun kubuce a yayinda fiye da 200 ke hannun 'yan Boko Haram din.

A sassa da dama na Nigeria, ana ci gaba da nuna kaduwa da kuma takaici kan faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Litinin.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a bidiyon da ya fitar ya ce kungiyarsu ce ta sace daliban nan 'yan mata su sama da dari biyu, makonni uku da suka wuce, ya kuma ce suna da niyyar sayar da su.

Karin bayani